Kamfanin BUA ya fitar da jawabi a matsayin martani ga zargin da kamfanin Dangote Group ke masa.

Kamfanin BUA ya fitar da dogon jawabi a matsayin martani ga zargin da kamfanin Dangote Group ya jefe sa da shi.
A wasikar da ta fitar ga duniya, BUA Group ya karyata Dangote, an dade Abdul Samad Rabiu yana ta gwabzawa da Aliko Dangote.
Kamfanin na BUA ya dauko tarihi tun daga 1991 lokacin da aka yi wahalar sukari, amma sai aka yi sa’a Abdul Samad Rabiu yana da sukari a kasa.
BUA ya ce Aliko Dangote ya nemi a saida masa sukarin, sai a karshe lamarin ya kare a kotu, kamfanin ya ce haka Rabiu ya jajirce na watanni uku.
Har ila yau, kamfanin ya ce ya taba karban aron fili daga Usman Dantata domin ya kafa kamfanin siminti, amma Dangote ya jawo aka karbe filin.
A dalilin wannan abin da ya faru a gwamnatin Olusegun Olusegun Obasanjo, BUA ya yi asarar filin da ya karbi aro daga hannun kawun na Dangote.
Wasikar ta ce haka kamfanin ya yi ta fama bayan samun lasisin kafa kamfanin siminti, BUA ya ce sam kalubalen nan ba su iya taka masu burki ba.