Advertisment
Tricks

Yadda zaka magance matsalar Unfortunately Application Has Stopped a wayarka

Shin Kana Fama Da Matsalar Unfortunately Application Has Stopped" A Wayarka?

Shin Kana Fama Da Matsalar Unfortunately Application Has Stopped” A Wayarka?

Ga Yadda Zaka Magance Matsalar “

Sau tari akan samu irin wannan matsalar a wayoyinmu na hannu musamman ma irin wayoyi London Use ɗin nan, sai kana cikin amfani da ita, kana shiga wani Application sai ta nuno maka “Unfortunately Application Has Stopped” dole haka zaka haƙura da Application ɗin daga ƙarshe ma sai dai ka gogeta, wasu kuma zuwa suke ana masu Plashing na wayar da sauransu.

To in sha Allah yau nazo maku da wata hanyar da zaku warware wannan matsalar cikin sauƙi.

Da zaran katura Application a wayarka kaje shiga cikinta sai tafara rubuto maka wannan turancin; “Unfortunately Application Has Stopped” to sai ka ƙwantar da hankalinka kaje Playstore ɗinka kayi search na sunan wannan App ɗin da take baka matsalar, idan tafito zakaga alamar ai kanada ita a wayarka, ma’ana dai bazasu sanya maka Installing ba saboda daman kanada ita sai dai zakaga Unstall da Open, to sai kayi Unstall ɗinta, bayan kayi sai kasake Installing nata kuma, zakaga tafara installing sabo, bayan tagama sai ka koma kaje ka sake shiga cikinta, idan still bata gyaru ba ta sake nuno maka wannan turancin. To karka gaji, sai kaje Setting na wayarka, kana shiga setting zakaga “Apps And Notification” sai kashiga, kana shiga zakaga ya bayyanar maka da duk Applications ɗin da suke a wayarka, to da zaran sun bayyana sai kabi a hankali kaje kan wannan Application ɗin da idan kaje shigarta take rubuto maka wannan turancin.

Sai ka danna ta, kana danna ta zakaga ta kawo ka wani wuri da aka rubuta “Clear Data” da kuma “Clear Caches” idan bakaga “Clear Data da “Clear Caches” ba to sai kashiga “Storage” kana shiga zaka gansu.

To kai tsaye sai kaje wurin da aka rubuta “Clear Caches” ka danna shi, kana danna shi zatayi Refreshing wannan Application ɗin, bayan tagama sai kaje ka sake shiga App ɗin, idan still ta ƙara rubuto maka wannan Turancin, to sai ka dawo ka danna “Clear Data“.. To daga nan fa in sha Allah idan ta gama Clearing, kana shiga App ɗin zai buɗe in sha Allah, domin zata wanke app ɗin ta dawo dashi sabo..

Sau tari wasu sukan rabu da waya saboda wannan matsalar kuma matsalar ba wata matsala bace.. Da yawan mutane suna shiga yan ƙananun matsaloli waɗanda gyaransu bai taka kara ya karya ba a waya amma daga ƙarshe sai dai su haƙura da wayar saboda rashin sani…

(Dr) Salisu Abdulrazak Saheel.

JOIN WHATSAPP GROUP FOR MORE

Advancement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advisement
Back to top button