Advertisment
Job/EmploymentTricks

Zenith bank: Yadda zaka Bude Account a bankin zenith Plc cikin wayarka

Yadda zaka Bude Account a bankin zenith Plc

Ayau muna tafe da yadda zaka bude bankin ajiya na zenith Bank cikin wayarka batare da kaje bankin ba kuma kayi amfani dashi wajan shigarwa da kuma fitarwa na kudi.

Zaka iya budewa a karamar wayar ko babba domin zakayi amfani da USSD code dinsu ne wajan budewa ba manhaja ba.

An kafa bankin Zenith Plc a watan Mayu 1990, kuma ya fara aiki a cikin Yuli na wannan shekarar a matsayin bankin kasuwanci. Bankin ya zama kamfani mai iyaka a ranar 17 ga Yuni, 2004 kuma an jera shi a hannun Nigerian Stock Exchange  (NSE) A ranar 21 ga Oktoba, 2004 biyo bayan babban nasar Initial Public Offering (IPO).

Dr. Ebenezer Onyeagwu shine mamallakin bankin zenith (CEO) tun ranar Saturday, March 25, 2023, har zuwa yau.

Abubuwan da ake bukata sune kamar haka:

• phone number: yakasance lambar wayar da kayi BVN da ita ce.

• Bank verification number BVN.

date of birth: yakasance date of birth dinka yayi wanda zaka saka yayi dede da wanda ke jikin BVN dinka.

 

yadda zaka bude bankin shine:

• da farko ka shiga phone din ka wato wajan da zaka tubuta lambobi kana shiga sai ka rubuta *966# wato USSD code na zenith Bank din.

 

• zai baka zabuka saika shiga zabi na 6 zai kara baka wasu zabukan saika danna number 1 wato zaka Budewa kanka account ne.

 

• zasu fada maka policy nasu gaba daya inhar ka amince saika danna yes wato number 1.

 

• zasu bukaci ka amince domin amfani da BVN dinka kana sakawa zasu nuna maka waje domin shigar da date of birth naka ka tabbatar DOB din yayi dede da wanda yake kan BVN din naka.

 

• daga nan zaka ci gaba domin bude account din kana kammalawa zasu turo maka account number ma SMS wato SIM CARD message.

JOIN WHATSAPP GROUP FOR MORE 

Advancement

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advisement
Back to top button